Wednesday, May 20, 2020

MUGUWAR KISHIYA littafin hausa

[
: MUGUWAR KISHIYA **** Part 1 **** Repost by AYS ZA Yau asabar gobe daurin auren Abbanmu umma tacewa Baffah? Nace Na'am Umma, Sai ta kira Sunan Kanwata Aisha, Sai ta amsa, Sai umma tac" saboda haka banaso kuyi wani abu da zaisa wani ko wata yace baku da tarbiyya inaso ku kasance masu nuna farin cikinku akan wannan al'amari, gaba daya muka amsa da cewa to umma "Tace allah yayi muku albarka, mukace amin, abbane ya shigo megadi na binsa da akwatuna, megadi ya aje ya fita, abba yace sannanku da zaman gida, Muka amsa gaba daya yauwa abba, yasa hannu yajanyo akwatunan nan ya bude kayane niki niki aciki yace hajiya wannan nakine, umma ta nuna farin cikinta sosai nida Kanwata aka bamu namu kayan amma fa mu bamu nuna farin ciki ba, Yau litinin kwanan amarya daya agidan abba, umma ta tura Ni da Aisha s Muje mu gaida amarya, Aisha ce tafara shigewa gaba muka shiga bangaren amarya muka tarar abba yana dakin Aisha tace aunty good mornng, amarya tajuyo ta kalli Aisha a wulakance tace ke dama a tsaye kuke gaida uwarku? Ni ne nace daga gaisuwa saiki zagi umman mu to wallahi badai uwarta ba, amarya tace kai dan uwarka ba'a koya maka tarbiyya ba? Nace badai uwata ba, amarya ta juya wajen abba alhaji yanxu kanaji yaronnan yana zagina? abba baiyi wata- wata ba ya daga hannu ya zabga man mari, Muka juyo a gigice domin abin ya matukar bamu mamaki kasancewar abba ko tsawa bayaso ayi muna amma da mamaki gashi yau shine ya daga hannunsa ya mare Ni, nan take Aisha ta fashe da kuka domin abin ya tsoratata, mukayo waje mu duka muna kuka, umma ta taho da sauri tatare mu tana tambayarmu lafiya? Aisha ce tayi mata bayanin abinda ya faru' abba ya fito a fusace yana ta kwala wa umma kira' umma ta amsa' abba yafara magana cikin fada, ke tsabar rashin mutunci shine zaki turo wadannan yaran naki suzo suyiwa amarya ta rashin mutunci? Umma tace alhaji anya kuwa acikin hayyacin ka kake? Ke ni kikeyiwa wannan tambayar to wallahi sai nayi maganinku duk wanda yace zai tabamin amaryata bazamu zauna lafiya dashiba agidannan, abba ya fice a fusace, duk abinda yake faruwa amarya tana tsaye tana yiwa umma dariya' Nine na xabura da niyar dukan amarya amma umma tai caraf ta rike hannuna tajamu mukayi daki muka bar amarya atsaye tana yimana dariyar mugunta amarya tace kadan kuka gani indai nice sai kunbar gidannan, KADUNA N,D,A Samar ya shiga damuwa matuka kasancewar rashin ziyarar da su abba basu kawo masaba kullum sukai waya da umma sai tace masa suna nan zuwa har ya gaji, dama ba,a maganar abbansa wanda idan ya kirasa baya daga wayarsa hakan yasa ya tambayi umma lafiya abba baya daga waya ta? Amma sai umma tace masa lafiya aikine yake hanashi kula da kiran da ake masa, duk da haka Samar yana xargin akwai abinda yake faruwa agidanmu dan haka yake ta fatan karasa shekara dayan data rage masa. a N.D.A domin yaxo gida yaga abinda yake wakana agidanmu, Umma ta gargadi mu akan kada mu sake mu fadawa yayanmu Samar halin da muke ciki kuma kada mu sanar dashi cewa abba ne ya hanamu zuwa visiting dinsa Abba ya shigo gida Aisha ta tashi domin tarar abbanta takarasa da sauri ta tsugunna agaban shi tace abba sannu da zuwa, ya juyo ya daka mata wata harara ke dalla can munafuka tashi ki bani waje Aisha ta tashi jikinta a sanyaye, umma wadda take zaune ranta yai matukar baci amma abinka da mai hakuri sai dai kawai tace allah ya kyauta axuciyarta, Aisha ta fada jikin umma tana kuka tana cewa umma me mukayiwa abba baya son ganin mu? Umma tace yi shiru kinji "yata ba laifinsa bane akwai makircin amarya acikin wannan shirin amma allah zaiyi mana magani, Aisha taci gaba da rusa kuka ba kakkautawa umma tana lallashinta, Na gama shirin makaranta kaf domin yaune zamu zana english waec dinmu naxo gurin abba ya tsugunna nace abba aban kudin makaranta abban namu ya kalleni sannan yasa hannu a aljihu ya dauko naira 30 ya mika mani, Nace abba ai 200 kake bani 30 baxata kaini ba, amarya ta daka mani tsawa kai!! Shashasha mahaifinka ya baka kudi kace yayi maka kadan? Abban namu ya kalleni sannan yasa hannu a aljihu ya dauko naira 30 ya mika mani, Nace abba ai 200 kake bani 30 baxata kaini ba, amarya ta daka mani tsawa kai!! Shashasha mahaifinka ya baka kudi kace yayi maka kadan? Abba yace kai tashi kaba mutane waje, Na tashi nayi waje, zuciyata cike da tsanar amarya, Amarya ta kalli abba tace Honey gobe kannena Zasu zo, abba yace su nawane? Su biyu ne kadai, abba yace to ai inbanda abinki kamata yayi ace sunfi haka yawa nan agidansu ne, amarya honey ai akwai wasu xasu xo suma amma sai nan gaba, abba yace to gskya yakamata suxo da fatiman nan da kike ta bani labari, amarya ai ita da abdul xasu xo, abba yace to allah ya kawo su lpy, ameen amarya tace, Can kuwa bangaren umma ba abinda take sai addu,ah akan allah ya warware kullun da amarya tayi akan mijinta da kuma allah ya mu hadu a whatsapp 09033627792 Group »Click Here And LIKE us On Facebook« »Click Here And Follow us on Twitter« ↓Help Your Self ↓ →»ku dinga comment →»yan mata da samari ayi invite →»dan momy na gaisuwa ↓Yauwa haka nakeso comment↓ class= class= class= Ayuba powar boy on-line 2.02 23:43 Can kuwa bangaren umma ba abinda take sai addu,ah akan allah ya warware kullun da amarya tayi akan mijinta da kuma allah ya dawo mata da babban danta Samar daga N.D.A lafiya Su fatima da abdul suka iso gate din gidan suka shigo kai tsaye domin alhaji ya sanarwa da mai gadi zuwansu, kana ganinsu kaga marasa tarbiyya, sukayi karo da Ni Alokacin ina kokarin fitowa daga gida' fatima ce tace kai makahon inane kanaji kana buge mutane? Duk da baisan gurinwa zasu ba sai nace allah yabaki hakuri, fatima taja wani dogon tsaki banza mahaukaci, Naji xafin kalmar sosai dan haka banyi wata-wata ba na daga hannu na sharara mata mari, ta kwalla wata kara ta tilasta umma da amarya fitowa aguje,suna zuwa suka taradda da abinda ya faru, umma ta tambaye ni Tace Baffah me ya faru na kwashe kaf abinda ya faru Nafada mata, amarya tace sam bazata yarda ba nan take dauko waya takira alhaji tace masa yai sauri yazo gida ba lapiya, ba'a dade ba sai ga alhaji yadawo, Ya taramu gaba dayanmu mutanen gidan, alhaji yafara magana kamar haka:- Kai dai wannan yaro anyi dan iskan yaro, yanzu ace kadaga hannu kamari kanwar amarya kuma kayi tunanin zan kyaleka to wallahi baka isa ba don haka ko ka tattara kayanka kabar gidan nan ko kuma ita uwar taka ta bar gidan, agigice umma tajuyo ta zaro idanu tace alhaji kasan me kake fada kuwa? abba yace ke kina nufin kice ni mahaukaci ne to abinda kunnenki yaji shi nafada, dan haka ku tashi ku bani guri, amarya da kannan ta suka tashi suna dariyar mugunta, alhaji ma yatashi yabisu, Ni kuwa tuni ya dauko jakar kayana abinka da mai xuciya, umma da Kanwata Aisha suka rike ni suna kuka, nima hawayen bakin ciki suka fara zarya a idanuna, Aisha kuka take kamar ranta zai fita Nayo waje nakama hanya batare da sanin inda zani ba, Umma da Aisha suna xaune suna ta rusa kuka, wayar umma ta fara ringtone Aisha ce ta duba wayar yayanmu Samar ne yake kira cikin hanxari ta daga tana shashshekar kuka hello! Yaya tace, a firgice Samar yace my sister lpy kike kuka??Umma tayi sauri ta kwace wayar daga hannun Aisha domin bataso Samar yasan halin da Muke ciki, tayi magana cikin karfin hali tace lpy lau Samar, Samar yacewa Umma Wai meke damun kanwata,? Umma tace tana kukane saboda rashin ganin ka akusa damu, Samar yace to inbanda abin sister ai saura wata bakwai nadawo, yace umma bata wayar na lallashe ta umma ta mika wa Aisha wayar tare dayi mata nuni akan tadaina kukan datake Aisha ta karbi wayar, yace sister kiyi hakuri kinji zan dawo nan bada dadewa ba, Aisha tace yaya wallahi kullum haka kake cewa, Samar yace to sister wannan karon dai tinda nace nakusa dawo wa to nakusa kinji? Tace to yaya, Samar yace yanxu kina Ss3 ko? Tace eh yaya, to ki maida hankali kinsan nurse nakeso kixama, tace to yaya, yace Baffah sun gama waec dinsu last week ko? Tace eh, yace to kice masa yadage sosai, tace to, yace yauwa sister bye, tace bye yaya, ya katse wayar, Can kuwa a bangarena tuni nayenke shawarar tafiya gidan kakannina na bangaren uwa dake unguwar Kaura na isa gidan na kwashe duk abinda ya faru na fada musu nan mahaifin umma yace kayi zamanka ko gidan kada ka kara zuwa ni zan dauki nauyin karatun ka shikuma abban naka xan neme shi, Ni kuma naci gaba da karatuna ba abinda yake damuna sai dai idan natuna halin da umma da Aisha suke ciki, a duk sanda mukai waya da yaya Samar sai naji kamar nafada masa halin da Muke ciki amma idan na tuna gargadin da umma tayi mani akan kada na kuskura na fadawa yayan namu, sai kawai nafasa fada masa, Amarya da kannenta abdul da fatima suna xaune a falo, abdul yace aunty nifa gaskiya yarinyar nan nake so, amarya tace wace yarinya? Abdul yace "yar kishiyar ki mana Aisha. ♥MU HADU A WHATSAPP♥ 08096831009 |ADINGA COMMENT| →YAN` MATA← ↓BIGBOY NA GAISUWA↑ →Copyrights← [7:36am, 4/24/2016] Bigboy 2: MUGUWAR KISHIYA *PART 2* RE POST BY AYS Amarya da kannenta abdul da fatima suna xaune a falo, abdul yace aunty nifa gaskiya yarinyar nan nake so, amarya tace wace yarinya? Abdul yace "yar kishiyar ki mana Aisha, amarya tace ai dama tunda naga take takenka nasan akwai magana, don haka kada kaji komai kamar ka mallaki Aisha ka gama, abdul yayi tsallen murna yace thank you aunty, fatima tace ikon allah ni banga abinso ajikin wannan yarinyar ba, amarya tace ina ruwanki? Fatima tace ba ruwana, Dare yayi abba yadawo ya shigo gida tare dayin sallama umma ta amsa tace ta tashi domin karbar kayan da suke hannusa, ya daka mata tsawa tare dacewa ina ruwanki da kayana? Umma taja da baya, abba yamika wa amarya kayan amarya ta karba' tare da yiwa umma gwalo, abba yajuyo yacewa umma duk da cewa yau kwanankine inaso kiyi hakuri domin yau adakin amarya nake son kwana, yajuya ya nufi dakin amarya batare da yatsaya jin amsar da umma zata bashi ba Bayan sun zauna shida amarya tace alhaji akwai maganar danakeso nafada maka, abba yace ina sauraronki, amarya ta gyara xama cikin kisisina tace dama wallahi yaron nanne abdul yace yana kaunar Aisha shine nikuma nace masa ya kwantar da hankalinsa kamar yasamune, abba yace ikon allah to ai Aisha "yarki ce kuma duk hukuncin da kika yanke akanta dai-dai ne, amarya tace yauwa alhaji shiyasa kullum nake kara son kasancewa da kai, abba yace nima haka, amarya tace amma yakamata kasanarwa da yarinyar da mahaifiyarta don kada inyi magana abin yazama rigima, abba yace nida "yata akwai wanda ya isa yayi min iko da ita don haka kice masa yasameta yayi mata magana, amarya tace nagode alhaji, Da safe abba yakwallah wa Aisha kira, ta amsa taho da sauri domin kuwa yanzu duk duniya ba wanda take tsoro sama da abba da kuma amarya, taxo ta tsugunna tace abba gani, yace saura wata nawa kigama secondry? Wata takwas abba, Abba yacewa Aisha to nayi miki mijin aure, agigice Aisha tace abba aure?? Abba yace eh kuma bawani bane sai wannan yaron abdul, abba bai tsaya jin amsar Aisha ba ya tashi yayi waje, umma wacce take jin duk abinda yake faruwa taxo ta kama Aisha suka shiga daki umma tai ta lallashinta, Aisha tace umma idan akwai wanda natsana aduniya bewuce amarya da danginta ba, gsky umma yakamata yaya Samar yasan halin da muke ciki, umma tace in banda abinki shima yayan naku ai akarshin abban naku yake, kuma in kin kwantar da hankalinki saura wata biyar yadawo kiyi hakuri, Aisha ta sake fashewa da kuka mai tsanani, Yau gari ya waye umma ta tashi tana cikin matsanancin zazzabi don haka tashirya domin zuwa asibiti, bayan abba ya shirya, suka taho shida amarya zata rakashi mota, tana tafiya tana ta wata yangar banza, umma ta karasa, tace yauwa alhaji dama so nake ka ajeni a asibiti, abba ya juyo yaharareta, yashiga motarsa batare daya kula da umma ba, yaja motarsa yana yiwa amarya bye bye itama tana yimasa, amarya ta juyo tayiwa umma dariya, umma tafito tanemi adai-daita sahu ta tafi asibiti, Aisha ta fito daga wanka matsanancin ciwon da kanta yake mata shiya tilasta mata xama akan gadon ta tayi tagumi hawaye ne yake gangarowa daga idanunta, jitai ana turo kofar dakin nata, ta tashi da sauri domin ta samu abinda rufe jikinta, amma kafin takai ga yin hakan tuni yashigo, abdul tagani yashigo yana mata murmushi, cikin fushi tace kai mahaukacin inane zaka shigowa mutane daki? Murmushi yaci gaba dayi tare da kura mata idanu, saikace mai kallon TV, kunya tagama rufe Aisha saboda daga ita sai daurin kirji, a hankali taga abdul ya fara matsowa kusa da ita, tafara ja da baya, tana bashi hakuri akan kada ya cutar ita, shikuwa dariyar mugunta kawai yake yana kara kusantar ta, Aisha tana ja da baya, shikuwa abdul yana kara kusantar ta hardai taje karshen bangon daki, abdul yayo kanta gadan-gadan, Aisha tana dubawa gefanta taga wukar da umma take amfani da ita, batayi wata-wata ba ta dasa hannu ta dauko wukar nan ta nuna abdul da ita, tace kada kamatso wallahi zan caka maka wukar nan, wanda tuni idonsa ya rufe yayo kan Aisha, ita kuwa batasan sanda ta labta masa wukar nan akai ba, abdul ya kwalla kara a zube akasa, amarya da fatima suka jiyo karar abdul su taho aguje, ita kuwa Aisha tuni ta rude sakamakon ganin yadda jini ke zuba daga kan abdul, su amarya suka karaso suna zuwa sukaga Aisha rike da wuka a hannu, basuyi jinkirin kiran abba ba tare da daukar abdul zuwa asibiti, Bayan sun karasa asibiti ne, likita ya fara duba abdul, su amarya da fatima suna zaune sunyi tagumi, alhaji ya shigo arude, ya nufi wajen likita, yace likita yajikin nasa likita yace da sauki, domin yanxu anyi masa duk abinda ya dace saboda haka zaku iya komawa dashi, alhaji yabiya kudin komai, sannan yadauko su a motarsa yana tafiya yana xage-xage akan Aisha, Amarya tana kara xuga shi, Ita kuwa Aisha tuni hankalinta yagama tashi domin sanin abinda zai biyo baya, tayo waje domin barin gidan kafin abba yadawo, tana zuwa kofa sukai karo da umma, umma tace lapiya Aisha? Aisha ta fada mata duk abinda ya faru' don haka umma tayi saurin bawa Aisha kudin mota, umma tace kiyi sauri kitafi gidansu kaka idan abin ya lafa saiki dawo, Aisha tace to umma, aiko min da kayana na makaranta, umma tace to, Aisha tayi waje, kana ganinta kasan arude take, Umma tana zaune tayi tagumi, taji shigowar su alhaji ko sallama babu sai masifa yake, yashigo dakin umma yatsaya akanta, yafara magana cikin fushi, Ke ina wannan "yar iskar yar taki? Maganar tayiwa umma xafi matuka, hakan yasa mikewa cikin fushi, tace alhaji duk abinda zakai kada ka kara kiran "yata "yar iska, ga "yan iska nan kana tare dasu wannan yaron yayi kokarin yiwa "yarka fyade amma kuma sai gashi kai kake kare......... Saukar mari umma taji a fuskar ta, tana dubawa taga amarya ce ta zabga mata mari, itama batayi wata-wata ba ta daga hannu ta sharara mata mari, abba dake tsaye yana kallo tuni shima ya daga hannu zabgawa umma mari wanda sai da ya tilastawa umma dafe kumatu, umma ta fashe da kuka mai tsanani wanda duk wanda yaji dole ya tausaya mata, alhaji ya kara da cewa kuma idona idan Aisha sai na karya ta, suka juya suka fice daga dakin suka bar umma tana kukan bakin ciki, Aisha bata tsaya ko ina ba sai gidan kakanninta ta fada musu duk abinda yafaru, hakan yasa kakanta yace gaskiya abin nashi cigaba yake don haka bari naje wajen malam nasanar dashi abinda yafaru, Bayan dare yayi amarya da abba suna zaune, abba yana ta lallashin amarya amma taki, sai abba yace kifadi abinda kike so nayi miki komai wahalarsa don ki daina fushin nan, amarya tayi murmushi da alama taji dadin maganar abba, sannan tace ni abu hudu nakeso, alhaji yace fade su duka indai kudi ke yinsu kamar angama ne, amarya tace 1 inaso kadawo min da yan uwana mutum takwas gidan nan da zama 2 inaso ka cika min alkawarina na motar da kace xaka sai min 3 inaso mufita kasar waje shakatawa, na hudun kuma baxan fada ba sai mun dawo daga shakatawa, abba yace wannan duk mai sauki ne indai zaki huce, don haka gobe zan tura driver ya dauko "yan uwan naki, mota kuma muna dawowa xaki ganta, don haka wace kasa. Kike so mu tafi? Amarya tace maleyshia, abba yace to kada kidamu tawan, farin ciki ya lullube ta, Abba ya gama shirin tafiya maleyshia shida amaryarsa gida kuma ya cika da "yan uwan amarya, wanda yanxu su goma ne tara daga ciki dukkansu maza ne majiya karfi daya ce mace wato fatima, sai sharholiyar su suke kamar gidan ubansu, umma kuma bata da damar sakewa haka umma tayi ta hakuri tana lissafin dawowar danta Samar wanda kullum takeyiwa addu'a, Yaune ranar tafiyarsu abba da amarya maleyshia don haka ya tara kowa nagidan, yafara jawabi kamar haka:- ♥MU HADU A WHATSAPP♥ 08096831009 |ADINGA COMMENT| →YAN` MATA← ↓BIGBOY NA GAISUWA↑ →Copyrights← [7:36am, 4/24/2016] Bigboy 2: MUGUWAR KISHIYA *PART 3* Yaune ranar tafiyarsu abba da amarya maleyshia don haka ya tara kowa nagidan, yafara jawabi kamar haka:- kamar yadda kuka sani yau zamu tafi, to don haka duk abinda kuke so ku tambayi wannan matar ya nuna umma, wadda kanta yake a tsugunne, yace kuma idan kika sake naji ance kin fita to allah ya isa, fatima tace alhaji yaushe kuma zaku dawo? abba yace bazamu wuce 3 weeks ba, aka raka su abba airport, bayan dawowarsu ne umma tafara fuskantar wulakanci kala-kala, badon allah ya isar da alhaji yayi akan fitar ta ba da ba abinda zai zaunar da ita A gidan, A kwana a tashi yau saura 2 weeks Samar ya dawo zaria domin yayi gagarumar nasara anan akayi posting dinsa ya kagu domin ji yake kamar ya janyo ranar domin yansan ganin su umma da Aisha da Ni, Rashin mutuncin da "yan uwan amarya suke wa umma ya tsananta, umma tana ta hakuri da jurewa, yau saura sati daya su abba su dawo daga maleyshia, Bayan dawowarsu abba da kwana daya abba ya siyowa amarya dalleliyar mota mai suna (BUGATTI) motar da a america ma kungiyar rich gang ne suka fara hawanta, idan ka hauta xa,ai tunanin governor ne, ya bawa amarya mukulli, tayi murna sosai ganin motar mai tsadane yasa taki hawanta tace sai ranar da zata unguwar kece raini, haka aka bar mota sabuwa kar a ajiye, umma tace to alhaji kacika min alkawari saura daya danace sai mun dawo, abba yace wanene? Amarya tace ya kira umma tukunna, abba ya kwalawa umma kira ta taho da sauri, tana zuwa ta tsugunna agaban abba, Amarya tace alhaji sonake kasaki wannan matsiyaciyar ta nuna umma, umma ta dago kai a da sauri, shima abba agigice yace saki!!!? Amarya ta fashe da kukan munafinci tace yanzu alhaji zaka iya karya alkawarina, abba yace yi hakuri, yanda kike so haka za ayi, yace wa umma nasake ki saki 1 batare da ya iya hada ido da ita ba, umma tafashe da kuka mai tsanani, wanda duk wanda yaji sai ya tausaya mata, amarya tasa kannen ta sukayita watsi da kayan umma, umma ta koma gidansu suka hadu gata ga Aisha ga Ni, Yau ne allah yayiwa Yaya Samar dawowa. NDA ya taho da "yan rakiya ta mota uku na sojoji, Ya dauko hanyar zaria, baisanar da umma yau xai dawo ba sakamakon yafison muyi mamakin ganinsa suna tafiya har suka shigo Zaria Suna tafiya a kan titi duk inda suka zo sai kaga motoci sun basu hanya, yana cikin dalleliyar motar da yasa aka yimai order kafin Yataho, motocin sojoji biyu abayana daya agabansa, kai idan kagansa bazakai tunanin soja bane, zakai tsammanin wani mai mulki ne, idan ka kalli jikin motar zakaga sunanta kamar haka:- [LAMBOGINY] Suka karaso unguwar suna shigowa yaga layin ya canza mashi gaba daya, jama'a kallonsu suke suna tunanin ina zasu tsaya suka karaso kofar gidanmu, sojojine sukai saurin fitowa su wajen, arba'in suka ka budemai mota yana fitowa suka kame, Suit ce fara ajikin Yayana Samar, yasa black shoe dinsa mai suna [deZaria] ya sa space mai farar kwalba, ga agogonsa, diamond, kana ganin dressing dayayi kasan kafin yazama soja nigger ne, ya kalli jama'a da suka cika wajen kallonsa kawai suke, Yaga abokansa dayawa aciki, take yakarasa cikin su suka gaggaisa sunata mamaki shikuwa tambayarsu yake, ya kowa da kowa? Suka amsa mai lafiya, yace bari nashiga naga su Aisha yanzu zan fito, sai yaga duk sunyi sororo, Yajuya ya sallami sojojinnan, suka nufi janguza barreck dake Sabon garin zaria shikuwa yagoya jakar sa, ya nufi kofar gidan mu, gadan gadan, Yana shiga yaji hayaniyar mutane yarabka sallama, mazane sun cika gidan, suka juyo suka kalleshi, bawanda ya amsa, suka ci gaba da abinda suke, ya wuce dakin umma yaga anrufe, sai ya tambayesu dan allah ina umma? kallonsa suke kawai ba wanda yacemai. Komai, waje yayo yashiga gidan su MEEMEE domin sune makotan kuma itace yarinyar dasuke mutunci a unguwarmu, tana ganinsa tazo da gudu dan murna, tafara cewa oyoyo oyoyo ga Samar ga Samar yayi murmushin karfin hali Yace wai bazaki girma ba, tace au hakama zakace? Mamansu suka fito suka tareshi da murna, yatambayesu ko umma ta sanar dasu inda xata? MEEMEE takalli mama yaga sunyi shiru, MEEMEE ce ta kwashe labari kaf ta fadamai, tuni yaji zuciyarsa tana tafarfasa' yayo waje MEEMEE tabiyoshi, suka shiga mota sai gidan kaka inda muke tare da umma, Suka karaso suna shiga sukai ido biyu da Aisha, a rude tace yaya Samar su umma da su kaka suka juyo umma Aisha da Ni ne muka taso aguje shima shararawa yayi da gudu Yakarasa inda muke' muka rungume juna kuka kawai muke, yace yanzu umma abinda yafaru akanku kenan amma bansani ba? Umma tace dana banaso natada maka hankaline, nan dai muka zauna aka kawo mashi abinci yaci amma abincin daci yake mai, saboda zuciyarsa tana ta saka mai yadda zan ramawa umma ta abinda akai mana, Bayan kakanmu yadawone yace min abinda nakeso da kai kada kayi wani abu domin yanxu kana yimata wani abu mahaifinka zai iya tsine maka, saboda haka dole a fara warware kullin data yi masa, MEEMEE ce tace nasan wajen wani malami mutumin kirki ne, ya juyo yace kada fa ki kaimu wajen boka, tayi dariya tace idan munje zaka gani, Suka karasa wajen malamin shida MEEMEE, makarantace babba, sukarasa akayi masu magana malam, suka gaisa yayi masa bayanin komai malam yace to abinda nakeso daku ga wasu ayoyi zan baku ku karanta su aruwa kubawa mahaifiyar taku, da sunyi ido hudu duk wani sihiri xai lalace, domin dama ansa masa kiyayyar tane aransa, sukai godiya suka ba malam abin sadaka suka kamo hanya, suna iso wa MEEMEE tayi abinda malam yace ayi ta bawa umma tasha, yamma tayi yadauko MEEMEE yakawo ta gidansu, Washe gari da safe suka nufi office din abba Shida umma suna zuwa suka shiga kai tsaye, abba yana rubuce rubucensa, sunayin sallama ya dago kansa yana hada ido da umma kawai sai gani mukai ya fadi kasa, da hanzari suka karasa yakama abba wanda tuni yasuma, suka dauki abba sai wajen malamin nan, suna zuwa malam yafara karatu akan abba, cikin kankanin lokaci abba ya mike kamar ba shiba, suka hada ido da umma yace hajiya tace alhaji yace me nake anan? Umma ta fashe da kuka, abba tuni hankalinsa yatashi, domin baisan abinda yasa Umma kuka ba, malam ne yayi masa bayani, akan komai, abba yayi kuka akamar karamin yaro, yarungume yaya Samar yana kuka tare da bamu hakuri, tuni malam yayi bayani akan saki 1 da abba yayiwa umma' aka daidaitasu, sukai addu'a suka tashi, abba yanufi office domin bai dakko motarsa ba, mukuma mukai gida, Tun muna mota umma taji ina waya ina cewa akawo min sojoji kurata mota uku, umma tace lpy? Yaya Samar yace umma inaso muna. Komawa gida ku koma gidan abba kedasu Aisha, umma tace to amma me zakai da sojoji? Yace umma inaso nayi musu hukuncine amma dan allah kada ki hanani, umma tace Samar in banda abinka ai hakuri shiyafi, yace umma nasani amma zuciyata bazata gafartaminba idan aka ci mutuncinki nakyale, ahaka dai umma ta yarda da abinda yace' muna karasawa gida su umma suka dauki kaya sai gidan abba, MEEMEE ce tajagoranci shigarsu umma gidan, suna shiga yan uwan amarya sukayo musu ca!!! Amarya ce taxo wajen umma tafara cewa mara zuciya ansaketa amma ta dawo, ♥MU HADU A WHATSAPP♥ 08096831009 |ADINGA COMMENT| →YAN` MATA← ↓BIGBOY NA GAISUWA↑ →Copyrights← [7:36am, 4/24/2016] Bigboy 2: MUGUWAR KISHIYA *PART 4* end Amarya ce taxo wajen umma tafara cewa mara zuciya ansaketa amma ta dawo, Aisha tayi caraf tace ke dallah can allah ya tona asirinki matsafiya kawai, fatima tace wa Aisha uwarki ce matsafiya, tuni Na daga hannu na zabgawa fatima mari nanfa fada ya kaure MEEMEE kokarin kare umma kawai take, Yaya Samar yana fitowa daga wanka yaji ana sallama dashi Yagama shiryawa kakin sojojine ajikinsa kamu nasa black spaces a fuskarsa, yana fitowa yaga kurata kowa da DG bellet a hannu sai muzurai suke, yayi wani murmushin mugunta yana xuwa kowa ya kame, suka hau motoci sai gidan abba, mutanen unguwa kuwa tuni kowa yafara dauko abin hawansa don ganewa idonsa HUKUNCIN yaya Samar, Suna zuwa ya sauko yakunna kai cikin gidan kurata suka takemai baya, jama'a kuwa sun taru sai kace taron daurin aure, yana shiga yaga wani yadaga hannu yana kokarin marin MEEMEE da take kare umma, saukar DG yaji abayansa, wanda hakan ya tilasta masa yin wani wawan ihu, nanfa kurata suka shiga aikinsu, ihun maza da mata kawai kake ji, nikuwa amarya na samu sai zura mata DG nake tana ihu, aikin kurata yayi tsamari domin kuwa aje DG sukai suka fara karyawa, duk wanda aka karya sai asashi a mota, amarya tayo waje aguje na bita tana zuwa tsakiyar layi nasa kafa na daki kafafunta tuni zube ta kasa tashi domin da alama itama ta karye, mutane sun zagayemu anrasa wanda zaice yi hakuri, motar abba ta faka, abba yafito da sauri yaxo yarikeni, wanda hakan yasa kurata tsayawa da aikinsu, amarya tasa hannu tarike kafar abba, abba yasa aka dauki amarya aka kaita gidan yan uwansu suma sauran can aka kaisu, suka kira mai dori yabisu daya bayan daya, Mukuwa muka dawo sabuwar rayuwa. Inda abba yasa akayiwa umma da Ni oder ta motoci guda biyu masu tsada, ita kuwa Aisha aka bata motar amarya (BUGATTI) dama amarya bata taba hawa ba, umma takira yaya samar tayi mai maganar aure, ya sunkuyar da kai domin bashi da ko budurwa, umma tace kayi shiru nyace umma ai bawata tsayayya, Aisha tayi caraf tace ga MEEMEE yajuyo na harareta, umma tace yauwa kanwarka tayi maka zabi, aikuwa haka akai tuni aka sanar da iyayenta, soyyayaya ta kulli, har aka sa rana amma ba asa da yawaba, don haka tuni ranar biki taxo aka sha gagarumin biki, abba yagina sabon gida su umma suka koma, shikuma shida amaryarsa Sukai barreck, rayuwa ta dawo mana sabuwa, Abba yaje gidan amarya, yana shiga yagata zama abin tausayi, ta taso tana rusa kuka tana neman gafara abba baiyi wata- wata ba ya mika mata ta kaddar saki, yajuya ya fita, amarya tabiyoshi tana neman gafara, amma ina tuni yashiga mota ya yo gida domin duk duniya ba wadda yatsana sama da amarya, kuma ba wadda yakeso sama da umma da "ya"yanta. Idan su umma suna zaune takan tunawa abba abinda yafaru cikin wasa amma abba sam baya so, Yaya samar shikuwa da MEEMEE ta soyayyar kawai suke shekawa. THE END Me zakuce game da wannan labarin? TAMMATBIHAMDULILLAHI GDY TA TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKIDAYA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFI Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 or 08067354033